
Babban Shugaban Kamfanin NNPC Ltd, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, tare da Shugaban Sanjiang Chemical Company, Mista Guan Jianzhong (hagu), da Shugaban Xinganchen (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd, Mr. Bill Bi (dama), suna sanya hannu kan Yarjejeniya (MoU) domin yin haɗin gwiwa kan Technical Equity Partnership (TEP) don taimakawa Wurin kammala da kuma gudanar da masana’antar mai ta Port Harcourt da Warri, a birnin Jiaxing, China, ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2026
Kamfanin NNPC Ltd ya sanya hannu kan Yarjejeniya (MoU) tare da kamfanonin Sin guda biyu, Sanjiang Chemical Company Limited da Xingcheng (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd, domin yin haɗin gwiwa ta hanyar haɗin gwiwar fasaha da hannun jari (Technical Equity Partnership – TEP) don kammala da gudanar da masana’antar mai ta Port Harcourt da Warri.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne ta hannun Babban Shugaban Kamfanin (GCEO) na NNPC Ltd, Injiniya Bashir Bayo Ojulari; Shugaban Sanjiang Chemical Company, Guan Jianzhong; da Shugaban Xinganchen (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd, Bill Bi, a birnin Jiaxing, China, ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2026.
Hakkan na kunshe ne a wata Sanarwa dauke da sa hannun Andy Odeh Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC Ltd.
A cewar Sanarwan, Tsarin haɗin gwiwar zai ƙunshi kammala sauran ayyuka a masana’antu biyu, tare da gudanar da su da kuma kula da su domin cimma ingantaccen aiki mai dorewa. Ana shirin faɗaɗa da sabunta masana’antu domin samar da kayayyaki masu tsafta da riba. Haɗin gwiwar na iya ƙunsar faɗaɗa ƙarfin petrochemical na masana’antu da kuma amfani da iskar gas da damar kasuwancin downstream ta hanyar kafa cibiyoyin masana’antu masu dogaro da gas.
Da yake jawabi bayan sanya hannu, GCEO na NNPC Ltd, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba, bayan fiye da watanni shida na tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin fasaha da na gudanarwa na NNPC da abokan haɗin gwiwar Sinawa, Sanjiang da Xinganchen.
Ya ce: “Dukkan ɓangarorin sun gane damar da za ta kawo riba mai dorewa ga kadarorin masana’antar mai na NNPC a Najeriya, da kuma muhimmancin haɗin gwiwa don samun nasara.”
Ojulari ya ƙara da cewa yarjejeniyar mataki ne mai muhimmanci a tafiyar neman abokan haɗin gwiwar fasaha da hannun jari domin sake farfado da kuma faɗaɗa masana’antar NNPC, tare da binciken damar petrochemical da masana’antu masu dogaro da gas.
Yarjejeniyar ta nuna niyyar ɓangarorin wajen ci gaba da tattaunawa cikin gaskiya, tare da samun cikakken tsare-tsare da za su biyo bayan samun amincewa da hukuma.


















