
Daga Bashir Bello, Abuja
Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin NNPC Limited, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR rahoton kuɗi na kamfanin na shekarar 2025 bayan an tantance shi (AFS), a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ojulari, wanda Babban Jami’in Kula da Harkokin Kuɗi na Kamfanin (CFO), Dapo Segun, ya raka, ya gabatar da rahoton wanda ya nuna sakamako mai ban sha’awa.
Wannan rahoton ya haɗa da ribar Naira Tiriliyan 7.2 bayan cire haraji (wanda ya nuna karuwar kashi 33% idan aka kwatanta da Naira Tiriliyan 5.4 a shekarar 2024), kuɗin rabon riba na Naira Tiriliyan 5.8 da kuma jimillar kuɗin shiga na Naira Tiriliyan 34.5.
A ranar 29 ga Satumba, 2026, kamfanin NNPC Ltd ta sanar da sakamakon kuɗaɗenta bayan tantance na shekarar 2025 da ta ƙare a ranar 31 ga Disamba, biyo bayan Babban Taron Shekara-shekara da kuma taron tattaunawa na biyu kan batun samun kuɗaɗen shiga tare da masana harkokin kuɗi da kasuwanci.
Sakamakon ya bayyana karuwar ƙarfin samun kuɗaɗen shiga na kamfanin da kuma ingantuwar yadda take gudanar da ayyukanta, lamarin da ke shimfiɗa harsashin ci gaba a nan gaba.



















