Shugaba/Babban Jami’in Gudanarwa, Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.
Kamfanin Sufuri Siminti na Dangote Cement yayi hubbasa wajen aiwatar da jerin shirye-shirye masu tasiri, masu dogaro da fasaha da aka tsara don inganta aiki, shugabanci da bin dokokin tsaron hanya.
Shugaban Sahen Sufuri na Kamfanin Siminti na Dangote Cement PLC, Mr. Murilo Silva
A wata Sanarwa daga Sashen Sadarwa na kamfanin ta ce ingantattun shirye-shiryen, sun ƙunshi manyan ɓangarorin aiki, ciki har da ƙididdigar aiki, ƙarfafa matakan shugabanci, da ingantattun tsarin ba da lamuni.
Ta ƙara da cewa shirye-shiryen sun haɗa da cikakken horon direbobi da haɓaka ƙwarewa, tsarin tsaro masu amfani da fasaha, ƙla’idojin tafiyar da tafiya, da kuma sake tabbatar da cancanta akai-akai.
Bugu da Kari Sauran ɓangarorin sun haɗa da gwajin shan ƙwaya na dole, haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyi, da kuma alƙawurran muhalli, zamantakewa, da shugabanci (ESG), shirye-shiryen Masu dorewa da shirye-shiryen da zasuyi tasiri ga al’umma, da sauransu.
Sanarwar da kakakin kamfanin, Anthony Chiejina, ya sanya wa hannu, ta tuna cewa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta yaba wa kamfanin kwanan nan bisa shirye-shiryen tsaro na gaggawa da yake aiwatarwa, wanda suka taimaka wajen rage afkuwar haɗurra a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta ruwaito Shugaban Sufuri na Kamfanin Siminti na Dangote Cement Plc, Mista Murilo Silva, yana cewa kamfanin ya ƙara inganta tsarin kula da sufurinsa ta hanyar tura fasahar duba ababen hawa ta atomatik da hanyoyin da ke amfani da bayanan sirri (AI) da nufin haɓaka ingancin aiki da tsaron hanya.
Mista Silva ya ce kamfanin ya tura ingantattun tsarin GPS da telematics don sa ido kan halayen direbobi kai tsaye yayin tafiya, wanda ke ƙarfafa sa ido da tsaron aiki a cikin motocinsa.
Hakazalika, Ya ƙara da cewa, don yaƙi da gajiyar direbobi, kamfanin ya ƙara neman lafiya direbobi, tare da gudanar da jerin tarurruka da masu motocin haya da direbobi don ƙarfafa wayar da kan jama’a game da tsaro, bin doka, da ɗaukar nauyi a hanya.
Mista Silva ya ce haɗin gwiwar kamfanin da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) tuni ya fara bada sakamako mai kyau, yana mai cewa haɗin gwiwar ta ci gaba da ƙarfafa ƙa’idojin tsaro a duk ayyukansa.
Ya ƙara da cewa jami’an FRSC suna shiga sosai wajen horarwa da tantance direbobi a Makarantar Koyon Tuƙin Motoci Masu Dogon Jiki ta Dangote da ke Obajana, inda suke bayar da jagorar fasaha, tabbatar da bin mafi kyawun ayyuka, da kuma tallafawa ci gaban direbobi masu ƙwarewa da sanin tsaro.
A cewarsa, adadin direbobin da ke shiga horo mai tsari, gwajin ƙwaya da barasa, da kuma sake tabbatar da cancanta lokaci-lokaci, ya ƙaru sosai, inda ya bayyana ƙaruwar a matsayin “babba ƙwarai”.
Ya ce, tsakanin zangon farko na shekarar 2025 zuwa 2026, Dangote Cement Plc, Obajana, ta samu gagarumin ci gaba a matakan bin dokokin tsaro, inda gwajin ƙwaya da barasa ya ƙaru da kashi 245.2, duba motoci kafin tafiya ya ƙaru da kashi 489.1, sannan shirye-shiryen horar da direbobi ya faɗaɗa da kashi 128.4.
Kwamandan Hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ya yaba wa kamfanin bisa kafa sabbin ƙa’idoji a fannin kula da tsaron hanya, kuma ya buƙaci kamfanin ya ci gaba da gyare-gyaren da suka ci gaba da inganta tsaro a fannin sufuri na Najeriya.
Kwamandan ya bayyana cewa idan aka kwatanta tsakanin 2025 da 2026, haɗurra da suka shafi motocin Dangote Cement Plc sun ragu da kashi 56, yayin da mace-mace ya ragu da kashi 36 kuma raunuka sun ragu sosai da kashi 52.

Shugaban Sahen Sufuri na Kamfanin Siminti na Dangote Cement PLC, Mr. Murilo Silva



















